Alhaji Yusuf Maitama Sule Ya Rasu

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano, Tsohon Jakadan Najeriya A Majalisar Dinkin Duniya

Dan Masanin Kano ya rasu ne bayan wata jinya a wani asibiti a birnin al-Qahira ta kasar Misra

Allah Yayi ma Dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, rasuwa yau litinin a bayan wata jinya a Misra.

Alhaji Maitama Sule, yana daya daga cikin jigogin siyasar arewaci da ma Najeriya baki daya, wanda ya fara siyasarsa tun a jamhuriya ta farko. Yana daya daga cikin wadanda suka fara kafa kungiyar da ta zamo babbar jam'iyyar siyasar Arewa, NPC.

Haka kuma, yana daya daga cikin jigogin da suka kafa jam'iyyar NPN a jamhuriya ta biyu, har ma ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar.

Ya taba zama jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya rike mukamai da dama na minista a gwamnatin tarayya.

A kasance da mu domin jin cikakken bayani game da wannan mashahurin dan siyasar na Najeriya. Allah Ya jikansa da Rahama, amin.