Rahotannin dake fitowa daga Maiduguri sun ce 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai farmaki kan garin maiduguri babban birnin Jihar Borno.
A yanzu haka an ce ana musanyar wuta da 'yan bindigar ta wajejen barikin Giwa.
Wasu rahotanni sun ce sun shiga garin ne ta hanyar Damboa, inda suka kutsa cikin wata unguwa mai suna Jiddari-Polo.
Yanzu haka dai mutanen unguwar sun gudu zuwa tsakiyar gari, yayin da wadanda suke zaune a yanzkin Barikin Giwa ma an ce sun bar gidajensu.
Sojoji sun dauki matakan tinkararsu.