Kasar Amurka, kasace daya da keda tsare-tsare masu kama da tsare-tsaren wasu nahiyoyi. A kasar Amurka kadai ne akanyi dokokin kasa, da gwamnatin tarayya ke shatawa, amma gwamnatotin jihohi nada hurumin kin bin dokokin, suna iya samar da nasu wanda sukan yi dai-dai da mutanen jihar su.
Wasu kadan daga cikin dokoki da ake da su a wasu jihohi, amma a wasu jihohi ba’a amfani dasu. A jihar Arkansas, karya doga ne mutun yaje gidan abinci ya danna hone na mota ko mashin, don hakan zai iya ba mutane tsoro. A jihar California, haramun ne mutun yayi amfani da leda don daukar cefane ko saka duk wasu abubuwa.
A jihar Colorado, kuwa an haramta ajiye kujeru a harabar gida, Su kuwa a jihar Florida, ana biyan kudin ajiyar dabbobi, kamar su doki, rakumi, giwa. Kamar yadda ake biyan kudin ajiyar mota a kan tituna. A jihar Georgia, kuwa karya doka ne mutun ya shiga jirgin ruwa har na tsawon kwanaki 30.
Jihar Hawaii kuwa karya doka ne mutun ya saka kudi a kunne, a jihar Indiana kuwa haramun ne mutun ya hau kan doki da tsayin shi yakai mita goma. Su kuwa a jihar Kansas, haramun ne mutun ya ci tayar mota. A jihar Kentucky kuwa babban laifi ne mutun yayi aure fiye da sau uku. Kamar ace mutun ya saki wata ya auri wata har sau 3.
A tsarin dokokin wadannan jihohin, idan aka samu mutun da karya daya daga cikin dokokin za’a hukunta shi, wanda zai iya biyan tara ko kuma zuwa gidan kasu, dai-dai da dokar da ya karya.