Bisa ruwayar Mujallar Faransa ta Football, tace Dan wasan gaba na kungiyar kwallo kafa ta Real Madrid, kuma dan asalin kasar Fotugal Cristiano Ronaldo, ne ya fi kwasar kudaden buga kwallon kafa, fiye da kowa a duniya a kakar wasannin kwallon kafa ta shekarar 2016, zuwa wannan shekarar da muke ciki ta 2017.
Inda ya kai labari da zunzurutun kudi wuri na gugar wuri, har Yuro Miliyan Tamanin da Bakwai da Dubu Dari Biyar. Hakan ce ta sa ya dara takwaransa Lionel Messi, dan kasar Agentina kuma gwarzon dan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta FC Barcelona.
Wanda shi kuma ya auna Yuro Miliyan Saba’in da Shida. Abokin wasansa dan kasar Brazil Neymar kuma ya zo na uku, da Yuro Miliyan Hamsin da Biyar. Neymar yana gaban dan wasan kasar Wales mai suna Gareth Bale mai bugawa Real Madrid, shi kuma ya soke Miliyar Arba’in da Daya a cikin burgamensa.
A wani gefen kuma, Jose Mourinho na Mancheter United, shine Kocin da ya fi samun albashi mafi tsoka. Mujallar tace a kakar kwallo ta 2016 zuwa 2017, ya sami Yuro Miliyan Ashirin da Takwas da Dubu Dari Biyar.