“Na canza sheka daga wakokin rauji da na soyayya zuwa wakokin addini” inji Yakubu Isa Wanda Aka fi sani da Emarcy, matashin ya bayyana haka ne yayi da yake tattaunawa da wakiliyar dandalinVOA a Kano.
Mawakin ya ce yana isar da sakonnin addini da soyayya ne, kuma a cewarsa idan ba’a isar da sakonnin soyayya da addini ba duniya ba zata zauna lafiya ba .
Ya kuma kara da cewa yana fatan kasancewa mawaki na farko a faggen wakokin adini a nahiyar Afrika.
Yakubu Isa, dai ya bayyana cewa ya soma da wakokin soyayya ne amma daga bisani ya canza akalar wakokinsa zuwa na addini, kuma ya ce shi mawakin R&B ne wato wakokin soyayya soyayya.
Daga karshe ya yi Karin bayanin cewa yana fadakar da alumma mahimmancin addini ga rayuwar dan Adam ta yau da kullum a kasancewar ya lura a nahiyar da yake mawaka sun fi ra’aja ne ga wakokin rauji ko na soyayya.
Your browser doesn’t support HTML5