Fiye da mata dubu goma da tamanin ne suke kamuwa cutar dajin bakin mahaifa a Nigeria

Hudu ga watan fabrarun kowace shekara, rana ce da kungiyar Lafiya ta duniya ta ware domin nazari da kuma fadakar da jama'a kai gameda illar cutar daji, dake ci gaba da halaka jama'a

Ranar hudu ga watan Fabrairun kowace shekara, rana ce da kungiyar lafiya ta duniya ta ware domin nazari da fadakar da jama'a gameda illar cutar daji dake ci gaba da halaka jama'a

Taken bikin bana shine"Zamu iya, nima zan iya" magance cutar.

Wani kididdiga da wata cibiyar dake aikin kokarin kawar da cutar ta cance a nahiyar Afrika mai suna Partnership for Eradication of Cancer in Africa ta fitar ya nuna cewa a duk shekara akwai kimamin mata dubu goma sha hudu da tamanin da tara da suke kamuwa da cutar daji ta bakin mahaifa, daya daga cikin cututtukan daji da take illa ga mata.

Kungiyar Lafiya ta duniya tace cancer bakin mahaifa itace cuta ta biyu dake kama mata, yan tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa arba'in da hudu a Nigeria.

A hira da wakilin sashen Hausa Babangida Jibirin yayi da Dr Mohammed Mohammed. Dr Mohammed yayi bayanin cewa cancer kan fito ne kamar kurji ko kumburi, yawancinsu, amma ba wai dukka dole sai ya zama kumburi ba.

Yace cancer ba kamar sauran cututtuka ba, maimakon ya daina toho, sai yayi ta toho, harma ya hana wasu sashen jiki yin aiki yadda ya kamata.

Dr Mohammed yace idan aka tare tsirowan yana fitowa, to ana iya samun nasarar warkar da shi, in ba haka ba idan ya kai wani mataki, to sai gyaran Allah domin da wuya a iya warkarwa.

Your browser doesn’t support HTML5

RANAR CUTAR SANKARA 3.15