Matasa Uku Sun Yiwa 'Yar Shekaru 13 Fyade

Wata kotu a jihar Katsina, 'karkashin jagorancin mai shara’a Fadila Dikko, ta bada umarnin a tsare wasu matasa uku da ake zargi da yiwa wata yarinya mai shekaru goma sha uku fyade.

Su dai matasan Aliyu Abubakar, mai shekaru ashirin da Ishaq Kabiru, mai shekaru goma sha tara da kuma Ibrahim Lawal, mai shekaru ashirin sun yiwa yarinyar fyade na tsawon wasu lokuta bayan da suka kulleta a wani shago mallakar 'daya daga cikinsu har tsawon kwanaki biyu a unguwar Tudun Wada a garin Funtua.

Dan Sanda mai gabatar da kara sufeto Kabir Muhammad, yace ana tuhumar matasan ne da hada baki domin aikata laifi, sacewa da tsare mutum da kuma aikata fyade, wanda yace ya sabawa sashe na 97,273,257 da na 283 da kundin dokar shara’a ta tanadar.

Daga bisa mai shara’a Dikko, ta bukaci a tsare su a gidan yari har zuwa ashirin ga watan Maris, a lokacin da za a saurari karar da kuma tura takardun karar zuwa ma’aikatar shara’a, domin samun shawara kan shara’ar.