Masu iya Magana dai sun ce tsabta cikon addini ce, kuma kamar yadda zamani ke ci gaba da kawo sauyi iri iri, matasa samari da ‘yan mata a birni da kauyuka na tafiya da wasu abubuwa na zamani kama daga nau’in sutura, takalma da sauran kayan kwalliya wadanda sukai dai dai da na zamani.
Koda shike yanayi na hunturu na bukatar kayan sawa masu nauyi fiye da lokacin zafi, kuma akan sami kura a wasu sassan arewacin Najeriya amma duk wannan baya hana matasa kwalliya musamman wata kwalliya da matasa sukai wa lakabi da wankan yamma.
Kamar yadda muka zanta da wasu ‘yan mata matasa akan wankan yamma kokuma kwalliyar yamma musamman a wannan lokaci na hunturu, da dama sun bayyana cewa sanyi baya hana su kwalliya har wadansu daga ciki suka bayyana cewa kwalliya tafi tasiri a lokacin hunturu domin a cewarsu hoda da sauran kayan shafa basa dadewa a fuska saboda zufa.
Samari a dama kan yi tattaki zuwa gidajen cin abinci ko shagunan Amani na sayar da kayayyakin tande tande ba domin komiba sai don nunawa juna kwalliya, kuma haka lamarin yake a bangaren ‘yan matan duk da cewa ba’a san malam bahaushe da irin wannan al’ada ba, amma zamanine ya zo da shi.
Domin jin ra'ayoyi mabanbanta dangane da wannan lamari na dabi'ar wankan yamma da fita shakatawa da yamma domin wasu dalilai, saurari cikakkakiyar hirar dandalinvoa a nan.
Your browser doesn’t support HTML5