Shahararren kamfanin bincike a fadin duniya “Google” sun bayyanar da yunkurin sun, na karfafa amfani da wutan lantarki da aka samar da ita ta hanyar rana ko iska.
A cewar babban mataimakin shugaban kamfanin Urs Holzle, sun iya gano cewar sabuwar hanyar samar da wutar lantarki, za tafi inganci da karfi wajen taimakama dakunan ajiyar bayanai da suke da su a ko ina a fadin duniya. Idan Allah ya kai rai shekara mai zuwa, suna sa ran komawa amfani da makamashin zamani dari bisa dari 100%.
Hakan zai taimaka matuka, wajen bama mutane damar bincike a kowane lokaci, domin mutane a ko ina sukan daura bidiyo, a shafin da yakai kimanin bidiyo dari hudu 400, a duk minti daya.
Inginiyoyin kamfanin, sun kwashe shekaru suna gudanar da bincike, wanda suka iya gano cewar wannan itace kawai mafita, idan za suyi amfani da wannan hanyar, domin kuwa zasu taimaka wajen yaki da matsalar dumaman yanayi a duniya.
Kamfanin dai tun a shekarar 2010, suka fara siyan wutar zamani, yanzu haka dai kamfanin shine kamfanin da yafi kowane kamfani a fadin duniya siyan makamashin zamani mai yawa.