Don Neman Gujema Cututtuka Masu Hadari, Nemo Gyada!

Gyada Mai Sihiri!

Gyada mai sihiri, a bara aga biyu, a murza aga hudu, badan tayi yaw aba, sai ‘yar sarki! Kirarin gyada kenan. Bincike ya tabbatar da cewar, ba kawai don dadi ya kamata a ci gyada ba, harma don samun lafiya. A duk lokacin da mutun yake sha’awar cin wani abun kwadayi, to kada ya wuce gyada, a cewar masana.

Domin kuwa tana taimakama jikin mutun, wajen nisantar cutar bugun zuciya. Binciken ya jaddada cewar idan mutun yaci gyada, da adadin ta ya kai kimanin cikin hannu a rana, babu shakka zuciyar shi zata samu garkuwa data kai kimanin kashi talatin 30% tsakanin ta da duk wasu cututtuka.

Haka kuma mutun zai samu garkuwa da cutar ciwon daji “Cancer” a turance, da kashi goma sha biyar 15%, kana da samun garkuwa ga duk wasu abubuwa da sukan haifar da mutuwa kai tsaye da kashi ashirin da biyu 22%.

A takaice dai, idan mutun yana cin gyada akai akai, zai samu lafiya mai inganci da kuma samun kariya ga wasu kananan cututtuka da kan shiga jikin mutun, a sanadiyar rashin cin abinci mai gina jiki, hakan na nuni da cewar, mutane su ci abinci mai gina jiki da kokarta cin ‘ya’yan gyada a kowace rana.