Kamaluddeen Kabir, mata shi ne, dan asalin jihar Katsina, an haife shi a garin Kaduna. Ya samu damar halartar makarantar firamare a Danmarna firamare dake Katsina, sannan yayi sakandire a kwalejin Barewa dake Zaria, daga nan ya sami damar cigaba da karatun Jami’a a Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato a inda ya kammala a shekarar 2009.
Kamaluddeen, yayi bautar kasa a Makarantar horon Ma’aikatan mai da ke Delta (PTI). Bayan ya Kammala aikin bautar kasa, ya samu aiki a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina, ya samu damar karo karatu a matakin digiri na biyu, a Jamiar Greenwich dake kasar Birtaniya, yasamu damar kammalawa a shekarar 2014.
Kamaluddeen ya samu damar komawa Birtaniya, don cigaba da digirin na uku watau digirin digir-gir “Ph.D” a fannin kimiyya da fasaha wanda a yanzu yana shekarar ta karshe.
Babban yunkurin shi, a rayuwa shine yaga cewar matasa a Najeriya, sun kai duk wani mataki da matasa suka kai musamman a kasar Ingila da ya gani ma idon shi, duk da cewar matasa a gida Najeriya suke da kason baya a wajen harka cigaba ta tallafi daga gwamnatoci da kamfanoni.