Sakina Mustapha Abubakar, wata matashya daga makarantar ‘yan mata ta Kabo, a karamar hukumar Kabo a Kanon Nieriya, ta kirkiri firijin na adana kayan gwari daga buhun algarara a wata gasar baje kolin fasaha na makarantun sakandare 600, da wata kungiya mai suna ‘White Horse risk management ta shirya a garin kano.
Dalibar ta ce, ta lura cewar mutane kan adana goro a buhun algarara na tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba, ta ce sai tayi tunanin idan har za’a iya adana goro na tsawon lokaci, zata gwada kirkirar wani abu mai kama da firijin domin adana kayan abinci na yau da kullum.
Ta hada firjin ne ta hanyar yanka katako tare da zagaye shii da buhun algarara inda aka zuba kayan gwari na tsawon lokaci ba tare da sun lalace ba.
Sakina, Dai na daga cikin dalibai da suka fi kowa hazaka a wannan gasa, baya ga firjin ma ta kirkiri tukunya cikin tukunya inda itama kamar firjin take domin adana kayan abinci na tsawon lokaci.
Your browser doesn’t support HTML5