Buri Na In Kashe Donald Trump

Donald Trump

Jami’an tsaro a Amurka, sun damke wani matashi mai shekaru ashirin da hudu mai suna Zachary Benson, bayan da ya rubuta a shafinsa na sada zumuta, cewa zai so ya ga shugaban Amurka mai jiran gado ya mutu.

Ya kuma rubuta a shafinsa na Twitter, cewa zai tarwatsa Amurka, na kuma kalle sakamakon zaben a talebijin.

Ya kara da cewa na tsaneku, inna so in tarwatsa duk wuraren zabe da duk inda kuke," buri na shine in kashe Trump, ban damu ba idan zan kare rayuwata a gidan yari" a cewarsa.

A yanzu haka Benson, na tsare a hannun ‘yan Sanda, inda yayi amai ya lashe yana mai cewa baya nufin abinda ya fadi yana kuma ladamar wadannan kalamai da ya rubuta, bashi da niyyar cutar da kowa kuma baya fatar wani abu ya samu shugaba mai jiran gado.