Daruruwan Matasa Sun Yi Zanga Zanga A Jihar Ondo

A yayin da ya rage kasa da mako daya a yi zaben gwamna a jihar Ondo, daruruwan matasa maza da mata da suka hada da dalibai, da ‘yan kasuwa sun yi wata zanga zanga a cikin birnin Akure, zuwa shalkwatar zabe mai zaman kanta a birnin Akure domin tilastawa hukumar zaben tsayar da dan takararsu Eyitayo Jegede maimakon Jimoh Ibrahim, da jam’iyyar PDP ta tsayar tun farko.

Shugaban matasan masu zanga zangar ya bayyana cewa dole ne su bayyanawa duniya cewa a bar masu dan takararsu Eyin Tayo Jegede ya tsaya takarar gwamnan jihar Ondo, kuma idan ya fadi zasu amince, amma idan aka hana shi takara, to baza su yard aba.

Kwamishinan zabe a jihar Ondo ya ce ba batun hukumar zabe bane, da zarar kotu ta yanke hukuncin cewa Eyitayo ne zai yi takarar gwamna a jihar ta Ondo, hukumar zabe zata bi umurnin kotu. Matasan dake dauke da kwalaye masu fubuce rbuce sun yi ta cika baki suna cewa idan ba Jegede ba. To babu zabe.

Zaratan ‘yan sandan kwantar da tarzoma, da sss da civil defence dauke da makamai, da mota mai sulke ne suka tare matasan kusa da ofoishin hukumar zabe ta jihar Ondo.

Ga rahoton Hassan Ummaru Tambuwar daga Akure.

Your browser doesn’t support HTML5

Daruruwan Matasa Sun Yi Zanga Zanga A Jihar Ondo