Sabuwar kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta jihar kano na yunkuri kawo wani sabon shiri da zai dawo da martaba da tarbiya a masana'antar kannywood.
Jarumi kuma furodusa Isa A Isa ne ya bayyana haka a wata zantawa da wakiliyar Dandalinvoa a Kano.
Jarumin ya bayyana babban kalubalen da ke ciwa masana’antar kannywood tuwo a kwarya bai wuci rashin tarbiya da girmama na gaba a harkar fina-finai ba, ya kuma kara da cewa a wancan lokacin da suka fara harkar fim shekaru 20 da suka gabata, masana’antar na da tsari sabanin yanzu.
Isa A Isa, wanda aka fi sani da Halifa ya bayyana cewa duk wadannan matsaloli da suke fuskanta sun samo asali ne ta hanyar daukar mutune masana’antar ba tare da cikakken bincike a kan inda mutum ya fito da irin tarbiyansa ba.
Ya kara da cewa, sabon shugabancin da suke da shi a yanzu ya fara kawo sauyi, domin canza irin kallon da alu’umma ke yiwa masu harkar fim.
Ga cikakkiyar hirar Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5