Wata dalibar jami’ar jihar Imo, Chinwendu Udensi, da abokanta suna hannun ‘yan Sanda, a jihar Rivers, biyo bayan shirin boge da tayi da wasu abokanta cewa anyi garkuwa da ita domin samun kudin fansa daga hannun mahaifinta.
Kwamishinan ‘yan Sanda jihar ya ce Chinwendu Udensi, ita ta shirya sace ta domin ta samu kudi daga hannun iyayaenta, domin a cewarta basu kula da ita kamar yadda ya kamata, tana mai cewa matsolanci ya yiwa iyayen nata kanta.
Wadanda suka saceta sun nemi a basu Naira miliyan shida, a matsayin kudin fansa, amma jami’an ‘yan Sanda, masu sai ido na ofishin sufeto janar na ‘yan Sandan Najeriya, a karkashin jagorancin Ben Igweh, suka kafa masu tarko inda suka ce a ajiye masu kudin a gadar sama na Obiri Ikwerre, a inda aka damke su.
Chinwendu Udensi, ‘yar asalin jihar Imo, tace bata jidadin halinda ta shiga ba, amma ta nemi gafarar iyayenta, ta kuma shawarci matasa ‘yan uwanta da kada suce zasu aikata irin abinda ta aikata domin bashi da alfanu.
Wata