Ga ma’abota sha’awar yawon bude ido a fadin duniya, ga wasu kadan daga cikin garuruwa masu kayatarwa, da duk wanda ke tunanin yawon ganin gari, ya kamata ya ziyaci wadannan garuruwan, a yankin kasashen turai. An tantance garuruwa da amfani da wasu abubuwa, da su keda na karin ilimi, da dunbin tarihi.
Babban birnin Prague, dake kasar Czech Republic, gari ne dake cike da kayan tarihi, da gine-gine masu ban sha’awa, duk wanda ya ziyarci garin sai ya kara marmarin zuwa. Birnin Copenhagen, dake kasar Denmark, gari ne mai dinbin tarihi, wanda suke da gidajen cin abinci da suke cikin jerin gidajen abinci, da su kafi haduwa a fadin duniya, garin kuma yana daya daga cikin garuruwa da su kafi tsadar rayuwa a fadin duniya.
Edinburgh, dake kasar Scotland, gari ne da ke dauke da wajajen tarihin duniya, garin nada asali tun a shekarar 1800, kimanin shekaru sama da dari biyu 200. Garin Zurich, na kasar Switzerland, gari ne da yake tsakiyar kasashen turai, gari ne da yake da iyaka da kasashe biyu, wanda hanyar jirgin kasan su na karkashin kasa yafi kowace hanyar jirgin karkashin kasa mafi tsawo a duniya, daga Zurich zuwa Milan.
Madrid, dake kasar Spain, gari ne dake dauke da dinbin tarihi, wanda tun zamanin annabawa, garin yake kuma har zuwa yanzu mutane na ciki, kana su kanyi wasu rayuwa ta irin mutanen wancan zamanin. Garin Bruges, dake kasar Belgium, gari ne da aka gina shi tun a karni na 12 zuwa 15, shekaru fiye da dubu daya. Garin Amsterdam, dake kasar Netherlands, kuwa gari ne da yake kewaye da kawa irin ta zamanin, kana da wasu gine-gine masu ban al’ajabi, abun dai sai wanda ya gani.
Wannan wata garabasa ne da idan mutun na bukatar yawon shakatawa da ganin duniya, sai ya shirya don cire kwarkwatar ido.