Barzil ta lallasa kasar Agentina daci 3-0 a gasar neman shiga cin kofin duniya 2018.
A cigaba da wasannin neman shiga cin kofin duniya Wanda za'ayi a shekarar 2018, a kasar Rasha Kungiyar kwallon kafa ta Colombia ta yi canjaras 0-0 tsakaninta da kasar Chile.
Brazil ta lallasa kasar Agentina daci 3-0
Venezuela ta samu nasara akan Bolivia da kwallaye 5-0
Uruguay tasha Ecuador 2-1
Paraguay bata ji da dadiba a gidanta daci 4-1 a hanun Peru
Yau kuma a nahiyar turai za'a gwabza ne tsakanin Armenian da Montenegro sai San Marino ta karbi bakuncin kasar Germany
France kuwa zasu fafata da kasar Sweden
England zata kece raini da Scotland
Romania da Poland
Sai Szech Republic da Kasar Norway
Northern Ireland ta kara da Azerbaijan
Slovakia zata marabci Lithuania yayin da Malta zata gwabza da kasar Slovenia
Ita kuwa Denmark da Kazakhstan.
Za'a fafata wasannin yau da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar da kamaru.
Your browser doesn’t support HTML5