Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Sweden mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Zlatan Ibrahimovic, ya nemi afuwa wajan magoya bayan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bisa dakatar dashi da akayi a babban wasan da kungiyarsa zata yi tsakaninta da Kungiyar Arsenal a ranar tara ga watan Nuwamba 2016, a gasar firimiya ta kasar Ingila.
Sakamakon dakatar da shi da hukumar kula da lig ta kasar Ingila ta yi saboda samunsa da akayi da katin gargadi (yellow card ) har guda biyar a jere.
Zlatan ya sami katin gargadi cikon na biyar ne a wasan da Manchester United ta yi da Swansea city a firimiya lig mako na sha daya a satin da ya wuce inda Manchester ta sami nasara akan Swansea da kwallaye 3-1.
A dokar lig ta kasar Ingila inda dan wasan ya sami wannan kati har sau biyar a jere to za a haramta masa wasa daya don haka ta fado masa a wasan da zasu yi da Kungiyar Arsenal.
Zlatan ya bukaci magoya bayansa da suyi hakuri su kwantar da hankalinsu ya kara dacewa ko baya cikin wasan yana da tabbacin akwai takwarorinsa 'yan wasa da zasu iya kai Kungiyar ga samun nasara a wannan babba wasan.
Ya kuma kara da cewa samun katin da yayi ba da gangan yayi ba kowa ya sanshi wajan duk abinda zai yi yakan yi ne da jikinsa kuma yanayin alkalan wasa na kasar Ingila ba kamar sauran kasashen bane.
Ibrahimovic na daya daga cikin 'yan wasan gaba da suke shan kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Manchester inda a yanzu haka ya jefa kwallaye har guda shida a wasanni daban daban.
Your browser doesn’t support HTML5