Gidauniyar dake tallafawa makarantun gaba da sakandare watau TETFUND, tayi alkawaringyara dakin karatu na jami’ar Jos, daya kone kurmus, biyo bayan wata mumunar gobara, a makonin da suka gabata.
Babban sakataren gidauniyar Dr. Abdullahi Baffa, ne ya bayana haka a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido jami’ar ta Jos.
Ya bayana takaicinsa kan irin barnar da wutar tayi yana mai cewa hakika ita wannan gobara tayi barna ba kadan ba duk littatafai, da kwamfutoci da sauran kayayyaki duk sun kone kurmus.
Shugaban jami’ar ta Jos, Farfesa Sabastine Maimako, yace duk da yake ba zai iya bada kiyasin dukiyar da aka rasa a wannan gobarar ba, sun dai bukaci manyan malaman jami’ar su bada Naira miliyan daya daya ya yinda sauran malamai da dalibai suma zasu bada tasu gudumawar.