Alamu Na Nuna Kamar Dan Wasa "Lionel Messi" Ya Fara Sanyi!

Dan Wasa Lionel Messi

Zuwa yanzu dai dan wasa Lionel Messi, ya saka kwallaye a raga, fiye da kwallayen da shahararrun ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Real Madrid su duka uku suka saka idan aka hada.

Dan wasan Barcelona nan dai ya samu nasarar saka kwallaye goma sha hudu, a wasannin goma sha daya 11 da ya buga, a farkon zamanin shi. Wanda suka fi kwallayen da 'yan wasa Cristiano Ronaldo, da Gareth Bale, kana da Karim Benzema, duk suka sakama kungiyar ta Madrid.

Duk dai da wariya da aka nuna ma dan wasan Messi, na ajiye shi a gefen fili na tsawon sati uku 3, bisa dalilin rauni da ya samu, yayi rawar gani ma kungiyar tashi. Dan wasa Messi abun fahariya ne, a cewar shugaban kungiyar Barcelona, Luis Enrique.

Dan wasan dai a wannan kakar bai fara da saka kwallaye ba, kamar yadda yayi a shekarun 2011 da 2012, inda ya fara da saka kwallaye goma sha hudu 14, a cikin wasannin goma 10, zuwa yanzu dai ya samu zura kwallaye takwas 8, kasa da kokarin shi a kakar da ta gabata.