Birnin Mumbai na kasar Indiya, inda kamfanin shirya fina finai na Bollywood yake da nada tazara daga yankin Kashmir, inda aka sami matsala tsakanin dakarun kasar Indiya, da masu tada kayar baya daga Pakistan, inda lamarin ya kai wani hali cikin makwannin da suka gabata.
Lamarin ya sa masana’antar shirya fina finai ta Bollywood ta zamo tamkar gidan kai ruwa rana, inda jaruman Indiya da na Pakistan suka sami rarrabuwar kawuna, jaruman Bollywood sun ce sun lashi takobin cewar baza su kara amfani da jaruman kasar Pakistan wajan shirya fina finai ba.
Haka zalika, a satin da ya gabata kuma hukumomi a kasar Pakistan suka hana nuna duk wani shiri na talabijin kokuma fim din Indiya a kasar wadda take da dinbin masu kaunar shirye shiryen Indiya.
Rashin jituwa tsakanin makwabtan kasashen ta kunno kai ne a sakamakon wani hari da wasu tsageru suka kai a kan wani sansanin sojin indiya dake Kashmir wanda yayi sanadiyyar rayukan sojojin Indiya ashirin.
Takaddama a kan hana jarumai daga kasar Pakistan fitowa a fina finan kasar Indiya ta dauki sabon salo ne a yayin da ake dab da fitowar wani sabon fim din soyayya na daya daga cikin manyan jiga jigan masana’antar kuma darakata Karan Johar, mai suna “Ae Hai Muski” ko kuma “Oh Heart, Its difficult” wanda zai fito ranar juma'a mai zuwa, inda jarumi daga kasar Pakistan Fawad Khan ya taka muhimmiyar rawa a ciki.
Your browser doesn’t support HTML5