Liverpool Da Manchester United Sun Ja Kunnen Magoya Bayan Su

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ta Manchester United, sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankulansu a lokacin da zasu kara a wasan frimiyaa ranar litinin mai zuwa a filin wasa na Anfield.

In dai ba'a mantaba a cikin watan maris da ta gabata hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA, ta hukunta kungiyoyin biyu bisa samunsu da laifin tayar da yamutsi a gasar cin kofin zakarun Turai Europa 2015/2016.

Kungiyoyin biyu sun fitar da sanarwa ta hadin guiwa cewar zasu gurfanar da duk wanda aka samu dea hannu wajan tada hayaniya a lokacin wasan.
Wannan karawa da kungiyoyin zasuyi a daren litinin ita ce ta 197 a tsakanin su.