Shararran dan wasan kwallon kafan nan na kasar Portugal kuma gwarzon dan wasan kwallon kafa na yankin turai mai taka leda a kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo, yace yana da yakinin cewa nan gaba zai iya kaiwa har shekaru goma masu zuwa yana fafatawa a fagen wasan kwallon kafa a duniya.
Ronaldo yace zai ajiye takalman taka ledansa a lokacin da yake da shekaru arba'in da haihuwa a yanzu Cristiano yana da shekaru talatin da daya a duniya.
Ya kara da cewa wanan shekaran tana daya daga cikin shekarun da yake ceke da farin ciki a rayuwar ganin cewa a shekaran yasamu nasaran lashe kofin zakaru na turai champion league da kuma kofin zakarun nahiyar kasashen turai wanda ya gudana a Faransa.
Haka kuma yana cikin na gaba gaba a cikin jerin sunan yan wasan da za'a zaba domin cin kambun zakaran dan kwallon duniya wanda ya taba riki wannan kanbin har sau uku.
Ronaldon ya bayyana hakan ne ayayin da yake bude wani sabon katafaran otel din da yagina a Lisbon.