Na'urar "Rosetta" Zata Watse A Cikin Tauraro Mai Wutsiya!

Na'urar Rosetta

A ‘yan kwanakin nan ne za’a kammala wani aikin binciken sararrin samaniya, da aka fara kimanin shekaru goma sha biyu 12, da suka wuce. A shekarar 2004, hukumar binciken sararrin samaniya ta kasashen yankin turai, “European Space Agency” suka tura wata na’uarar bincike mai suna “Rosetta” zuwa duniyar wata.

Na’urar Rosetta zata karbi sako a zangon karshe, daga matattarar bayanai dake cikin sararrin samaniya, a garin Darmstadt, a kasar Germany, ranar Juma’a. Ana sa ran za’a bayyanar da duk wasu bayanai da na’urar da kwaso a tsawon shekaru da tayi a cikin duniyar watan.

Duk dai da cewar, a iya tsawon shekaru da na’urar tayi a sararrin, ta bama mahukunta damar fahimtar abubuwa da dama, da yadda rayuwa take gudana a sararrin na samaniya.

Na’urar ta samu damar daukar hotuna da suka kai kimanin dubu tamanin, wanda sukayi dai-dai da murabba’in wuri milliyan dari bakwai da talatin. Daya daga cikin abun da ya bayyana a cikin abubuwa da aka fahimta, a cikin zaman na’urar a sararrin shine.

A cikin sararrin samaniyar, an iya fahimtar yadda iskar da mutane ke shaka don rayuwa, tasamo asali da yadda take gudana a cikin jama’a. Haka kuma a sanadiyar wannan na’urar an iya gano cewar akwai ruwa a cikin duniyar wata, duk dai da cewar ba irin ruwa na wannan duniya bane.