Manchester City Ke Gaba Akan Teburin Firimiya Lig

 Pep Guardiola

Pep Guardiola

Dan wasan kungiyar kwallon kafa na Super Eagles, Kelechi Iheanacho, wanda kuma yake taka leda a kungiyar Manchester City, na Ingila, ya ce yana samun kwarewa a karkashen Pep Guardiola.

A yanzu haka dai Kelechi, ya jefa kwallaye ukku, a wasani ukku, yana mai cewa yana jin dadin wannan ci gaba da yake samu a kungiyar ta Manchester City, kamar yadda ya shedawa shafin yanar gizon kungiyar.

Manchester City, dai ta doke Bournemouth, da kwallaye hudu da nema, yana mai cewa “ zan ci gaba da yin aiki tukuru a kowace rana a kuma kowane wasa kuma zai yi amfani da dama idan ta samu”.

Dan shekaru goma sha tara yace abinda ke gaba yanzu shine wasan da zasu buga da Swansea. Ya kara da cewa yana farin ciki nasarorin da suka samu, da hukumomin kungiyar da kocin da sauran jama’ar kungiyar.

A yanzu Manchester City, ne ke kan teburin firimiya lig, da maki goma sha biyar daga wasani biyar.