Twitter Ya Tsunduma Cikin Harkar Bidiyo

Twitter

Shafin sadarwa na Twitter ya tsunduma cikin harkar bidiyo sosai, inda ya fitar sanarwar wata sabuwar manhaja kyauta ga masu na’urar kama tashoshin talebijin har da Apple TV da Amazon Fire TV da kuma na’urar wasanni na Xbox.

Tweitter dai zata baiwa duk masu amfani da ‘daya daga cikin na’urorin damar kallon hoton bidiyon da yake akan shafin Twitter harma da na wasu abokan hadin guiwarta, cikin harda tashoshin wasannin kwallon kafar Amurka, guda goma da kallon labaran tashar Bloomberg da dai sauransu.

Masu amfani da na’urarin kuma zasu iya ganin sakon da yafi ‘daukar hankalin jama’a da aka rubuta a shafin Twitter, da hotan bidiyo da ya fi daukar hankali.

A cewar kamfanin Twitter duk mai amfani da na’urar kama tashoshin Talebijin idan har yana da wannan manhajar zai iya kallo ko da kuwa bashi da shafin Twitter yazo na kansa.

Wannan yunkuri na Twitter yazo ne a kokarin da take yi na kasancewa kafada da kafada da sauran hanyoyin sadarwa na zamani a yanar gizo.