Yau Take Sallah

Yau Take Sallah

Jama'a, a bisa al'ada wayewar gari bayan hawan Arafat, shine Sallar Eid-Kabir, wace ake kira Sallar Layya.

Mutane a fadi duniya, sukan je sun sallaci raka biyu domin murnar wannan rana wanda daga bisani liman zai yanka Ragon sa bayan yayi huduba a bayan an sallaci raka biyu na sunnah kamar yadda aka umurta ayi.

Duk a ci gaba da shagulgular sallah, yara kan ziyarci 'yan uwa da abokan arziki a wani abu na al'ada da ake kira yawon sallah.