Masana gandun daji tare da sanin dabi’un namun daji, sun bayyanar da wani yunkuri da gwanatin kasar China, tayi wajen samar ma tsofaffin dabbar daji Panda. A wata kasida da masanan suka gabatar a birnin Honolulu, inda suka bayyanar da yunkurin na gwamnatin China, duk dai da cewar sauran dabbobi kamar su gwaggon biri, suna fuskantar barazana a cikin gandun dajin.
Masanan na ganin cewar, dumaman yanayi na daya daga cikin matsalloli da Panda, zasu fuskanta a nan gaba, wanda hakan na iya zama sanadi na rashin yawaitar dabbar a doron kasa.
Sun kuma bayyanar da tsoro da suke da shi, na yadda ake farautar sauran namun daji a wasu kasashe, suka kara da cewar a cikin gandun dajin kasar Congo, da wasu kasashe a yankin sahara, haka da kasar Indonesia, suna matukar farautar wasu daga cikin nau’o’in birrai, wanda hakan zai iya kawo karshen wasu nau’in birrai da ake da su a fadin duniya.
Sun kara da kira kan cewar, sai an tashi tsaye wajen kare gandu daji, da tsirran da suke cikin su, don taimakama yanayi da kan tallafa ma rayuwar dan’adam.