Ana gab da kammala jirgin ruwa da yafi kowannen girma a fadin duniya. Wani hamshakin mai kudi dan kasar Swedziland Mr. Meraviglia, shi ke da kamfanin katafaren jirgin. Ya bayyanar da cewar nan batare da jimawa ba, za’a gama hada jirgin da duk abubuwan alatu, da suka kamata ace jirgin ruwa na da shi, kamin a fita yawon shakatawa da shi, na tsawon awowi goma sha biyu.
Wannan jirgin zai dauki kimanin sama da mutane dubu biyar da dari bakwai a lokaci daya, idan wannan jirgin ya kammalu zai zama jirgi na farko da yafi kowannen girma a tarihin duniya da ya shiga cikin ruwa.
Yanzu haka dai an fara siyar da tikiti na shiga jirgin don yawon shakatawa, ga duk wanda ke da bukata, duk a cikin jirgin akwai otel na alfarma, kasuwa, filin wasanni, da dai duk wasu abubuwa da suka kunshi rayuwar dan’adam. Ga duk mai bukata, tikitin na farawa ne daga dala dari tara da talatin $930 dai-dai da naira dubu dari uku da talatin.