An umarci mata da su tabbatar da ganin cewa sun rungumi ilimi, domin kyautata rayuwarsu da na ‘ya’yan su domin ci gaban al’umarsu.
Hafsa Mohammad ce ta furta haka a hirar su da wakilyar Dandalin voa Baraka Bashir, matashiya wace ta kammala jami'ar a Ahmadu Bello dake Zaria ta ce ta fuskanci matsaloli da dama a yayin da ta ke makarantar da suka dangancin rashin hadin kai daga bangaren malamansu.
Ta ce akwai rashin daidaito idan suna da wata matsala suke kuma so a dora su a hanya, akan nuna musu kabilanci da fifiko, ko da yake malama Hafsa ta ce ta so ta zama Nurse amma hakan bai yiwu ba,
Ta kara da cewa duk da hakan bai hana mata neman ilimi ba, inda daga bisani ta bukaci ‘yan uwanta mata da su tabbatar da ganin cewa sun maida neman ilimi wajibi garesu domin kyautata rayuwar su da ta iyalansu.
Ita dai Hafsatu ta fara da kwalejin Sa'adatu Rimi, ne kafin daga bisani ta samu gurbi a Jami'a, yanzu da ta kammala bata shawa'ar aikin gwamnati illa ta sami sana'ar kanta tunda babban bukatar ta, ta yi boko.
Your browser doesn’t support HTML5