Kananan Zaurawa Cikas Ga 'Yan Mata

Matasan 'Yan Mata

A zauren mu na mata a yau, mun sami bakunci wata matashiya Asma'u Sani wacce ta ce yan mata na kokawa ga dabi'un kananan zawarawa da basu da shekaru masu yawa na hana musu rawan gaban hantsi, inda ta ke cewa kawo yanzu samari sun fi damawa da su, a cewarta a duk lokacin da saurayi ya bukaci da su rakasu unguwa ba sa cewa a'a.

Wanda haka ke taka muhimmiyar rawa wajen samun na kashewa daga wajen samarin nasu, don ba dukkanin lokuta ba ne suke samun raka su wata unguwa da suke son zuwa.

Tana mai cewa idan zaurawan suka fito sun samn yadda zasu gyara kansu har ma sun fi wasu ‘yan matan gogewa, sun san yadda zasu sati man shafawa mai kyau, suyi kwalleya a gansu kamar ‘yan mata, ga kuma kaya suna ganin sun tara.

Ta kara da cewa zaurawa sun fi ‘yan mata samun kudi kuma tilas ne su fi ‘yan mata sayen kayan kwalliya.

Asama’u, ta kara da cewa idan saurayi ya sami bazawara kuma ta iya soyayya kudin da zata samu ba kadan bane a cewarta kowane saurayi zai yi tunanin cewa yadda ta faranta masa shima bari ya faranta mata.

Ta ce samarin yanzu idan har budurwa na son karfafa dankon soyayya abinda kike so ayi maki shine idan saurayi ya bukaci a raka shi unguwa za’a bishi wannan sai zaurawa zasu iya, domin idan budurwa ta fita ta dade za’a yi ta yi mata waya daga gida ana ina kike su kuwa zaurawa a’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaurawa Cikas Ga 'Yan Mata - 3'51"