Ministan ma’aikatar matasa da wasani na Najeriya Solomon Dalung, ya umarci hukumar kula da kwallon kafa NFF, data biyar mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa na Flying Eagles, Samson Siasia, albashinsa na watani biyar.
Ministan ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar da Siasia, ya kai masa a Ofishin sa dake Abuja.
Siasia, dai shine ya jagoranci ‘yan kungiyar Flying Eagles ‘yan kasa da shekaru 23,zuwa wasani Olympics, na bana a kasar Brazil, inda kungiyar ta lashe Tagulla a matsayi na ukku.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya din NFF, ta ce bata ga wata takarda da ta fito daga hannun Samson Siasia, ba mai nuna cewa yana bukatar barin aiki, inda ake rade raden cewa Siasia, ya rubuta takarda ga hukumar na neman ajiye aikinsa, saboda rashin biyansa albashin san a watanin biyar.
Sai dai dama shi Siasia, kontraginsa zai kare ne bayan dawowa daga gasar Olympic, da aka gudanar a kasar Brazil.
Your browser doesn’t support HTML5