Hattara Da Kalamai Mawaka

Ibrahim Uba Abdullahi K' Arrow

An bukaci mawaka dasu san irin kalaman da zasu kasance suna amfani dasu wajan wake waken su na fadakarwa da nishadantarwa.

Wani mawakin Hip-Pop na hausa Ibrahim Uba Abdullahi K_arrow , wanda suke wakar tare da abokinsa ya ce sun shafe shekaru goma sha hudu a wannan sana’ar.

K-arrow ya ce yawan kallon wakoki ne ya ja hankalinsu wajnn fara waka don su tunatar da alumma dangane da abubuwan da ke faru a tsakanin alummimsu.

ya kara da cewa daga cikin abinda ya kara hasasa burin nasu akwai wata rana wasu suka zo neman masu rap na Hausa hakan ma ya taimaka a'inun wajan jajircewa da yin wakokinsu a harshen Hausa

ya ce sun fuskanci kalubalen da dama a lokacin da suka fara waka, wanda da zarar sun fito daga gidajensu suka dinga fuskanta tsangwama daga mutane, amma hakan bai sa sunyi kasa a guiwa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Hattara Da Kalamai Mawaka - 5'26"