WASHINGTON D.C —
'Yan Sanda a jihar Imo, sun ceto wani jariri dan kwanaki ukku da haihuwa daga hannu wasu barayi yara su biyu.
Sun saci yaron ne kimani awowi 48, bayan haihuwarsa a wani asibitin a karamar hukumar Isiala Mbano, a jihar.
Kwamishina ‘yan Sandan jihar Taiwo Lakanu, wanda ya tabbatar wa manema labarai batun ya ce da samun labarin sai jami’an ‘yan Sanda, suka bazama aikin neman mutane cikin hukumci obangiji aka cafke su.
Ya kara da cewa barayin yaran Ngozi Anyanwu, da abokiyar laifinta wace ba’a anbaci sunan ta ba suna daf da sayarda jaririn ne jami’an ‘yan Sanda, suka cafke su.
Mahaifiyar jaririn, Uchechi Ekwedike, ‘yar shekaru 21, ta ce matar ta yaudare tane domin ta sace mata jariri, tuni aka mika wa iyayen jaririn dansu