Ofishin jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Borno ya tabbatar da rasuwar wani daga cikin jami’an hukumar a sakamakon fadawa cikin ruwa a yayin da jami’an hukumar ke kokarin kama wani dillalin kwayoyi.
Ranar litini babban kwamandan hukumar na jihar Borno, Mr Ona Ogilegwu ya bayyanawa kamfanin dillancin labarun Najeriya afkuwar lamarin a yayin da jami’an suke gudanar da aiki a Gwanke dake Maiduguri.
Kwamandan ya kara da cewa jami’ai hudu ne suka fada cikin kogin Gwanke a lokacin da suke kokarin kamo wanda ake zargi da dillancin kwayoyin, ya ce jami’an sun sami matsalar ne a sanadiyyar rashin iya iyo a ruwa. Daya daga cikinsu ya rasa ransa ne a asibiti yayinda ake kokarin ceto ransa, an kuma sallami sauran da lamarin ya rutsa da su daga asibiti.
Shugaban jami’an ya ce hukumar baza ta yi kasa a gwiwa ba wajan tabbatar da zakulo wanda ake zargin a duk inda yake da kuma gurfanar da shi.