Mata A Maida Hankali Ga Ilimi Ba Kyalkyalin Duniya Ba

Rabi'a Nasidi Ahmad

An shawarci mata dake makarantun gaba da sakandare da jami’oi, dasu zage damtse wurin gudanar da harkoin neman iliminsu domin samun nasara a rayuwa.

Wata dalibar jami’ar Bayero dake Kano, Rabi'a Nasidi Ahmad, wace ke matakin karatu na ukku, a jami’ar ne ta bada wannan shawarar a wata hira da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir a Birnin Kano.

Matashiya wace ke mataki na ukku a jami'a Bayero ta Kano, ta ce a lokacin da ta kammala makarantar sakandare ta shiga kwalejin share faggen shiga jami'a wato college of art and Islamic studies inda daga nan ne ta sami shiga jami’ar Bayero.

Ta hankalin yan uwanta mata da su maida hankali wajan neman abinda ya kaisu jami’a, maimaikon mai da hankali wajan kyalkyalin duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata A Maida Hankali Ga Ilimi Ba Kyalkyalin Duniya Ba - 3'59"