Koch Din Super Eagles Zai Fara Aiki Da Mataimaka Ukku

A model presents a creation by Cypriot-born Turkish fashion designer Hussein Chalayan during his 2019 Autumn / Winter collection catwalk show at London Fashion Week.

Ana sa ran cewa sabon Koch din kungiyar kwallon kafar Super Eagles Gernot Rohr, zai kama aiki a Najeriya da mataimaka na masamman har ukku.

Wadanna mataimaka sune mai bashi shawara, mai nazari akan hotunan bidiyon wasani da mai horar da ‘yan wasa afanin motsa jiki.

Rohr, ya rattaba hannu a kwantaregin shekaru biyu ne kuma ana zato cewa shi zai biya mataimakan da zai dauka domin taimakamasa.