Hankalinsu Yafi Raja'a Akan Kudi

Kungiyar Ghana Blackstar

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar ta kasar Ghana George Afriyie, yace 'yan wasan Blackstar na wannan zamanin, ba don kishin kasar suke takawa kasar leda ba ko kuma soyayyar yiwa kasar wasan bane sai dai sun fi nuna damuwarsu ga kudaden da za’a basu.

Ya ce hankalin 'yan wasan yafi raja'a ne akan ladan nasara mai tsoka da kuma kudin shiga wasanni da kasar zata basu.

Ya kara da cewa 'yan Ghana da dama ne suka bayyana damuwarsu ga yadda 'yan wasan Blackstars suke nuna son kudi fiye da kasar kuma wannan yayi sanadiyar kungiyar ta Blackstars tana rashin magoya baya.

George Afriyie yace bukatar da 'yan wasan keyi na a biya su dollar Amurka, dubu goma na ladan wasa na tabbatar da maganarsa, koda yake ma’aikatar wasanni ta rage kudin daga dollar Amurka, dubu goma zuwa dubu takwas.