‘Yar wasan tsalle tsallen Amurkar nan Simone Biles ta sami zinari na hudu a gasar wasanin Olympics na shekara ta dubu biyu da goma sha shida a gasar motsa jiki a kasa.
Biles, yar shekaru goma sha tara, tafi kowacce mace fice a tarihin gasar olympic. Ranar litinin ta sami tagulla a gasar tsayuwa kan gora, wani tashin da bai zo mata da dace ba, kasancewa babu macen da ta taba samun zinari biyar a gasar Olympic daya.
Wadansu mata hudu sun sami zinari hudu a gasar cikin shekara guda.
An kyatata zaton Biles zata lashe gasar motsa jikin, yayinda abokiyar karawarta Aly Raisman ta sami azurfa.
A gasar tsere kuma,Jason Kenny ya sami zinari, karo na uku a wasan Olympic na bana.
Brazil ta sami zinari a gasar kwallon hannu a gabar teku, ta doke kasar Netherland.
Dan wasan tseren kasar Jamaica Usain Bolt ya fara wani zagayen gasar neman zinari, a gudun fanfalake na mita dari biyu da aka fara jiya talata, da za a kammala gobe alhamis.
An ba Bolt lakabin mutumin da yafi kowa sauri a duniya ranar lahadi lokacin da ya yiwa ba’amurken nan Justin Gatlin fintinkau a tseren mita dari.