Wani Dalibi Yayi Kira Ga Gwamnati Da kuma Karin Haske Akan Miyagun Ayyukan Da Yajin Aikin Malaman Jami'ar Ke Jefa Dalibai

Wani dalibi dake karatu a jami’ar Niger Delta (NDU) yayi kira ga gwamnatin jihar Bayelsa da ta sake duba bukatun kungiyar malaman jami’a dangane da matakan yajin aikin da ‘ya’yan kungiyar suka dauka.

Mujallar Daily post ta bayyana cewa da yake Magana da manema labarai, wanda ya jagoranci tawagar kungiyar daliban jami’ar Iboteme Mathias, ya yi wannan kira ne a wani taron gaggawa da kungiyar daliban ta kira.

Ya yi tuni da cewa ‘ya’yan kungiyar malaman sun amince janye yajin aiki idan gwamnati ta biya su bashin albashin watanni biyu da suke binta.

A jawabinsa, ya kira ga gwamnati ta yi la’akari da irin yanayin da daliban ke ciki domin a cewarsa dalibai ne ke fama da matakan da kungiyar malaman ta dauka tun ranar 26 ga watan afirailu akan rashin biyansu albashi da gwamnati ta yi.

Dalibin kuma dan gwagwarmaya ya yi Magana akan kisan wani dalibi mai koyon harkokin kere kere mai suna Obele Wilson, wanda wasu tsageru suka harba da bindiga a Yenagoa makonnin da suka gabata a matsayin daya daga cikin ire iren da lamarin da yajin aikin ya haifar.

Ya kuma yi Magana akan yawan mugayen ayyukan da wasu daliban ke aikatawa a yayin da wasu daga cikin dalibai mata suka shiga harkar karuwanci da kuma mugayen ayyukan da takwarorin su maza suka shiga aikatawa.

Yayi kira da gwamnatin jihar ta saurari kukan daliban ta amince da bukatar kungiyar malaman na biyansu albashin watanni biyu.

Dalibin ya bayyana cewa matsalar babbar barazana ce ga jihar Bayelsa da kuma Najeriya baki daya, domin a cewarsa makaratar wadda ke wuri mai sarkakaiya ta taimaka wajan rage ayyukan tsageranci, amma tun daga fara yajin aikin, yace sun ga karuwar aikata ayyukan tsageranci na fasa bututan mai da sace mutane domin kudin fansa, duk a samakon rashin aikin yi.