WASHINGTON, DC —
Tsohon dan wasan Super Eagles Jay Jay Okocha, ya shawarci ‘yan kwallon da suka wakilici Najeriya, a gasar Olympic da cewa su yi alfahari da kasancewa suna wakilitar kasar su fiye da sun samun kudi.
Ya ce koda yake takawa Najeriya, leda kadai ba zai sa suyi arziki ba sai dai kawai domin karrama kasar haihuwa.
A baya dai ‘yan kungiyar sun yi barazanar kauracewa buga wasani a ci gaba da kasar Olympic da ake gudanarwa a Rio de Janeiro ta kasar Brazil.
Ya kara da cewa takawa Najeriya leda zai sa a san mutun a fagen ta’maula, kamar yadda ya ce zuwan sa Jamus domin taka leda ya kawar mashi da iyalansa talauci, wanda hakan ya faru ne saboda yayi fice a lokacin da yake takawa Najeriya leda.