Evgeny Tishchenko Ya Ci Lambar Zinari A Damben Mafiya Karfi

Evgeny Tishchenko na Rasha, ya ci lambar zinari ta damben mafiya karfi a wasan Olympic, bayan da ya doke Vassiliy Levit na kasar Kazakhstan, a gasar da aka kusan yin kunnen doki, ta yadda ma har sai da 'yan kallo su ka yi ta ihu ga alkalan wasan, saboda shawarar da su ka yanke kan gasar.

Ga alamar Levit ya fi burgewa a mafi yawan lokacin wasan, to amma dukkan alkalan uku sun ba da nasara ga Tishchenko da ci 29 akasin 28.

A gasar tsaren keke na maza kuma, Elia Viviani na kasar Italiya, bayan da aka dauka shi kam shikenan tunda ya fadi yayin tsaren, to amma sai kawai ya zaburo, har sai da ya ci zinarin.

A gasar ta jiya Litini har ila yau, an yi na bangaren juye-juyen gabobi da jiki.

Shahararriyar 'yar wasan nan ta Amurka Simone Biles, ta yi ta tangadi kan sandar juye-juye, ta yadda kiris ya hana ta zama mace ta farko da ta ci lambobin zinari biyar a jere a gasar Olympic guda. Biles ta ci tagulla a gasar.

Sanne Wevers ta kasar Netherlands ce ta ci lambar yabo ta zinari a gasar juye-juye bisa sandar, yayin da kuma Laurie Hernandez ta Amurka ta ci lambar yabo ta azurfa.