RIO 2016: Dan Najeriya Ke Kangaba A Wasan Boxing!

Dan wasa Efe Ajagba

Efe Ajagba, dan Najeriya, mai wasan “Boxing” ya samu nasarar doke abokin hamayyar shi, jim kadan bayan fara wasa. A cikin dakika ashirin da uku 23, da fara wasan Efe, yayi ma abokin wasan nashi nushin lahira kusa, inda abokin karawan nashi ya bada gari.

Zuwa yanzu dai dan wasan na Najeriya, ya doke ‘yan wasa biyu da na kasar Trinidad, da Nigel Paul dan kasar Tobago, da ke dauke da kambun dan wasa da yafi karfin hannu na kilo casa’in da daya 91Kg.

Efe, shi ke wakiltar Najeriya, a wasan boksin, ya dai taba zama zakara a gasar wasan kasashen Afrika a shekarar 2015. Haka a shekarar 2014, lokacin da yake dan shekaru ashirin da biyu, ya lashe kyautar Tagulla, a gasar kasashen mallakar Turawa, wanda aka gwabza a Glasgow ta kasar Ingila. Duk cikin gasar babu wanda yayi nasara da dukan lahira kusa sai kasar Najeriya.

Yanzu haka dai dan wasan zai samu damar zuwa wasan zagayen karshe, ida zai hadu da shahararren dan wasa Ivan Dychko, daga kasar Kazakhstan ya Talata.