Usain Bolt, Ya Zama Wanda Yafi Kowa Gudu A Wasannin Rio

Mutumin da yafi kowa gudu a duniya ya samu lambar yabo sau uku a jere a gudun fanfalaki na tsawon mita 100.

Mashahurin dan tseren nan na kasar Jamaica Usain Bolt, ya yi wa dan kasar Amurkan nan Justin Gatlin fintikau duk da yake Gatlin na gaban sa a tashin farko a jiya lahadi a gasar da akeyi a Rio de Jeneiro na kasar Brazil.

Dubun dubatar mutanen dake kallon wannan gasar ta allon talabijin a garin su Usain Bolt sun barke da sowa lokacin da suka ga ya wuce Ba-Amurken nan Gatlin ya isa shingen a cikin dakika 9.58 kasa da adadin lokacin kundin tarihin wannan gasar.

Yayin da Gastlin dan Amurka yazo na biyu sai dan kasar Canada Andre de Grasse yazo na ukku da lambar azurfa bronze.

Sai dai kafin wannan tseren mita 100, dan kasar Africa ta Kudu Wade Van Niekerk, ya kafa tarihi a gudun mita 400, wanda ya kammala a cikin dakika 43.03 inda ya doke mutanemn biyu dake biye dashi wato kirani James, na Grenada da Lashawn Merrit na kasar Amurka.

Duka-duka dai anci gwal 22 a gasa 12 da akayi jiya lahadi.