Ku Shirya Arangama Da Boko Haram, Buratai Ya Fadawa Sababbin Hafshoshin Da Aka Yaye

Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai a jawabin da yayiwa matasan sojoji dari biyu da makarantar horas da hafsoshin soja ta yaye, ya bayyana cewa ba maganar ragantaka a aikin soja, dan haka ya yi kira da cewar matasan hafsoshin su kasance cikin shiri a kowane lokaci domin fuskantar ‘Ya’yan kungiyar Boko haram.

Babban jami’ain ya yi wannan jawabi ne a wajan bikin yaye daliban hafsoshin kwanaki kadan bayan bude sabon mazaunin makarantar horas da manyan hafsoshin a Jos dake jihar Plateau, kuma ya kara da cewa wajibi ne matasan su kasance masu yawan motsa jiki domin kasancewa masu kuzari a kowane lokaci.

Ya kuma tunatar da jami’an cewa sojin kasar sun taka rawar gani a Najeriya, kuma kasar tana alfahari da su, dan haka yayi kira ga sabbin hafsoshin da su kasance masu kishin kasar su, da kuma sadaukar da kawunan su domin alfahari da aikin nasu.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa babban hafsan dakarun ya bayyana cewa ganin irin matsalolin tsaron da kasar take fuskanta musamman a arewa maso gabashin kasar dake fama da matsalar boko haram, wajibi ne dakarun su kasance masu kuzari kuma cikin shiri a kowane lokaci.

Daga karshe ya kara da cewa gaskiyar ita ce, dole ne dakarun su zama cikin shiri domin zasu iya ganin abubuwan mamakin da basu taba tsammani ba a arewa maso gabashin kasar, kama daga kwanton baunar bazata, da kuma kananan bama baman da ‘ya’yan kungiyar boko haram suke dasa wa da sauransu.

Dan haka ya ce matasan zasu zama abin dogaro a matsayin su na hafsoshi, dan haka ya zama wajibi su kiyaye dokokin aikin su da kuma kasancewa masu azama da kuzari, daga karshe ya kara mai maita cewa babu ragantaka a aikin soja.