Jam'iyyar Adawa Na Gaban ANC Ta Gwamnati A Zaben Afirka ta Kudu

Jami'an zabe

Sakamakon zaben da akayi a kasar Afrika ta kudu ya nuna cewa jam’iyyun adawa na kan gaban jam’iyya mai mulki ta ANC.

:

Yayinda aka kirga kusan fiye da rabin kuri’un, jam’iyyar ANC ce ta ke da kuri’u mafi yawa a fadin kasar, amma duk da haka wannan shine kuri’u mafi kankanci da ta taba samu tun karshen mulkin nuna wariyar launin fata a shekarar aluf dari tara da cisi’in da hudu.

Dama kwararru sun yi hasashen cewa jam’iyyar ANC ba za ta sami goyon baya ba sosai a wannan shekarar, saboda kasar na fama da matsalar rashawa da kuma yadda jama’a ke nuna rashin amincewarsu akan karancin ababen more rayuwa.

Masu kada kuri'u

Jam’iyyar dai na da tabbacin cewa ita zata lashe mafi yawan kujerun majallisun garuruwa da biranen kasar. Amma, jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance tana kan hanyar ci gaba da rike majalissar birnin Cape Town sannan tana keke-da-keke da jam’iyyar ANC a majallisun biranen Johannesburg da Pretoria.