An Cafke Wasu Matasa 'Yan Fashi

Hukumar ‘yan Sandan jihar Legas ta cafke wasu ‘yan fashi da makami da suka dade suna addabar jama’ar Ajangbadi da Shibiri dake karamar hukumar Oto-Awori a jihar ta Legas.

Wadanda suka shiga hannu sun hada da Emeka Emwis, dan shekaru 25, Eze Ikasuana dan shekaru 24, da Kabiru Sadiq mai shekaru 22.

Kakakin ‘yan Sandan jihar SP Dolapo Badmus, wanda ya tabbatar da afkuwar lamari ya ce wasu ne da suka tsallake rijiya da baya ne suka tseguntawa jami’an ‘yan Sanda lokaci da ‘yan fashin ke gudanar da ta’asar su kafi ‘yan Sandan suyi masu kofar rago su danke su .

A cewar kakakin wadannan matasa da aka cafke ‘yan wata kungiyar ‘yan fashi ne da ake kira “One Million Boys Gang”, ya kara da cewa an samu Bindiga kiran gida da Adduna da suke amfani dasu wajan gudanar da fashin su yana mai cewa da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu a gaban kotu.