Kalubalen Ku Kamfanonin Arewacin Najeriya

Sagiru Muhammad

A shirinu na nishadi a yau bakuncin mawaki Sagiru Muhammad muka samu wanda aka fi sani da mai lallaiyo , mawakin a fagen shirya fina-finan Hausa wanda ya shafe fiye da shekaru goma a harkar waka.

Yace yaje kasashe da dama kuma wakar ce ta kai shi, yana mai korafin cewa kamfanoni dake tallata kayayyakinsu basu son yin amfani mawakan hausa.

Ya kuma kalubalanci kamfanomnin arewacin Najeriya da suka damka talace talacen kamfanoninsu ga mawakan kudu baya suma zasu iya yana mai cewa duk aikin fasaha ce.

Har ila yau a fagen mu na tsegumi muna nan dai tare da Sagir da mawakan u Mai lallaiyo wanda ya ce Sabon album dinsa mai suna Bahaushe , da Dodon gona da kuma dukiya na nan tafe nan ba da jimawa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Kalubalen Ku Kamfanonin Arewacin Najeriya - 4'15"