Wata kotu a Ado-Ekiti a jihar Ekiti tasa a tsare wani matashi dan shekaru goma sha tara da haihuwa mai suna John Julius, a gidan yari saboda zargin da ake masa na yiwa wata mata ‘yar shekaru talatin da biyar fyade.
Dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Bayo Ajiboye, ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 12, ga watan yulin nan da muke ci a garin Efon Alaaye-Ekiti, a lokacin da matar ke kan hanyarta na komawa gidan daga gona.
A cewar ma gabatar da kara laifin ya sabawa sashe na 358 karami sashe na 16, na dokar jihar Ekiti, ya kara da cewa matar a yanzu haka tana asibiti ana yi mata magani saboda raunukan da matashi ya ji mata.
Alkalin kotu Modupe Afeniforo wace ta bada umarnin a tsare shi ta dage sauraren karar sai 19, ga watan Agusta na wannan shekaran.